Ana ta sukar afuwar da aka yi wa Alamieyeseigha

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Gamayyar kungiyoyin farar hula dake yaki da cin hanci da rashawa da kuma ke fafitukar tabbatar da shugabanci nagari a Nigeriya sun nemi shugaba Goodluck Jonathan da ya janye afuwar da ya yi wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka yi a birnin Abuja, kuma sun ce za su yi zanga zangar lumana domin nuna rashin amincewa da matakin da shugaban kasar ya dauka.

Kungiyoyi da mutane dabam daban a Najeriyar dai na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu game da wannan ahuwa, koda a jiya ma wasu jam'iyyun adawa sun shiga sahun masu sukar matakin da shugaban kasar.

Jam'iyyar adawa ta ACN ta ce ahuwar ba wani kyakkyawan misali ba ne ga al'umar kasar.

'ya bamu mamaki'

Jam'iyyar ACN ta ce ta dade ta fadan irin raunin da gwamnatin kasar ke da shi amma wasu kawai na ganin sukace kawai irin ta yan adawa.

Ta ce ahuwar da gwamnatin ta yiwa tsohon gwamnan Bayelsa ya fito da kura-kuren gwamnatin kasar a fili.

Alhaji Lawal Shauibu, sakataren jam'iyyar ACN ta kasa ya ce; " Gaskiya wannan al'amari ya bamu mamaki."

"Wannan mataki zai kara ingiza mutane ne su shiga cikin cin hanci da rashawa.

"An ce shugabanci a rika yin shi da misali saboda masu tasowa su san abun da yake daidai." In ji Lawal Shauibu.

Gwamnatin Najeriyar ta ce an gabatar ne a gaban Majalisar kolin kasar kafin a amince da ahuwar.