Xi Jinping ya zama shugaban kasar China

Image caption Xi Jinping Shugaban kasar China

An samu sauyi a babban birnin kasar China Beijing, inda majalisar dokokin kasar a hukumace ta zabi Xi Jinping a matsayin shugaban kasa.

An dai yi zaben ne bisa al'ada saboda Xi ne dan takarar jami'ar kwaminisanci da aka zaba domin zama shugaban kasar.

Yan Majalisar dokokin kasar ne da su ka kusan kai dubu uku su kayi zaben a babban dakin taro dake Biejing domin tabbatar da Xi a matsayin shugaban kasar.

Zaben dai bai zo da mamaki ba ganin cewa sunan XI ne kadai a takardar kada kuri'a da Jam'iyyar kwamisinanci mulki ta fitar.

Har wa yau 'yan Majalisar dokokin sun zabi Liu Yaunchao a matsayin mataimakin kasa.

A baya dai Liu ya nemi sauyi a shugabancin kasar ta China, amma a yanzu haka mukamin na sa bai bashi karfin fada a ji ba.