Kungiyar Kasashen Musulmi ta nemi hadin kan Paparoma

Pope Francis
Image caption Kungiyar Musulmi ta duniya ta nemi kyakyawar alaka

Kungiyar Kasashen musulmi ta OIC ta bayyana fatan ta, game da samun kyakyawar alaka tsakanin addinin Islama da kuma na Kirista karkashin Sabon Paparoma Francis ,fiye da yadda aka gani a lokacin magabacinsa Pope Benedict.

A wata wasikar ta ya murna da Shugaban Kungiyar ya aikewa sabon Paparoman, ya ce yana fatan samun kyakywar alaka da kuma aminci

Tunda farko dai Jami'ar Al Azhar dake Masar tace tana bukatar ganin alaka kyakyawa tsakanin addinan biyu

Wani mai magana da yawun Al Azhar ya ce a shirye jami'ar take ta dawo da tattaunawa tare da fadar Vatican, bayan sun dakatar da duk wata hulda a shekarar 2011 a lokacin da Al Azhar din ta zargi Pope Benedict da rashin mutunta addinin Islama

Karin bayani