Cece-kuce kan yiwa Alamieyeseigha afuwa

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce bai ji dadin yadda gwamnatin kasar ta yi afuwa ga tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha ba, wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.

A wani sako da ya fitar a shafinsa na Twitter, ofishin ya ce: "Yana kallon matakin a matsayin wani koma-baya ga yunkurin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar.

A makon nan ne gwamnatin Najeriya ta sanar da yin afuwa ga Alamieyeseigha da wasu mutane shida a kasar da suka hada tsohon dan takarar shugaban kasa marigayi Shehu Musa Ya'aradua da marigayi Janar Oladipo Diya.

A farkon wannan makon ne shugaban Godluck Jonathan ya bayyana a wajan taron majalisar tsaro ta kasa cewa za'a yi wa mutanan afuwa.

Tun wannan lokacin ne kuma kungiyoyi da 'yan sisaya a kasar ke ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan mataki da gwamnatin ta ce zata dauka.

Inda har wasu kungiyoyin farar hula su ka yi barazanar yin zanga zangar lumana har sai gwamnatin ta janye wannan mataki.