Za'a koma ba 'yan tawayen Syria makamai

Taro kan 'yan adawar Syria
Image caption Faransa da Burtaniya na son a rinka baiwa 'yan tawayen Syria makamai

Shugaban Faransa ya kare shirinsa na baiwa 'yan tawayen Syria makamai, a daidai lokacin da masu fafutuka suke bikin cika shekara biyu da fara tarzomar nuna adawa da gwamnati.

Da ya ke magana a wurin taron kungiyar Tarayyar Turai, Fracois Hollande, ya ce 'yan tawayen sun bayar da tabbacin cewa makaman ba za su fada hannun wadanda basu dace ba.

Faransa da Burtaniya na neman Tarayyar Turai ta janye takunkumin shiga da makaman da ta sanya wa kasar ta Syria.

Sai dai kasar Jamus ta ce har yanzu bata yanke hukunci kan ko za ta amince da hakan ba.

Akalla mutane 70,000 ne aka kashe yayin da miliyan daya suka kauracewa gidajensu.

Sai dai kuma wasu kasashen na kungiyar tarayyar Turai na dari-dari da wannan shiri na Faransa da Birtaniya, inda wasunsu ke ganin cewa, tallafawa 'yan tawayen Syria da makamai ba zai ahaifar da komai ba illa kara dagula rikicin.

Su dai Birtaniya da Faransa suna so ne su samu damar bada makamai ga dakarun 'yan tawayen Syria domin a ganinsu yanzu, an shiga tsaka mai wuya a kasar, inda idan har aka cigaba a haka, babu bangaren da zai samu nasara.

Kuma a hakan za'a cigaba ne kawai da zubar da jini.

Karin bayani