Matakin ceto tattalin arzukin Cyprus

Bankin Cyprus
Image caption Bankin Cyprus

Jama'a a Cyprus sun maida martani cikin fushi game da labarin dake cewa masu ajiya a bankuna ne za su dauki nauyin biyan dala biliyan sha ukun da aka amince dasu a Brussels a matsayin kudaden tallafafi domin ceto tattalin arzikin kasar.

Mutane sun yi ta cire kudadensu daga injinan cirar kudi inda suke iyawa; an kuma yi ta cire kudi daga banki daya kachal da aka bude a yau--shi ma kuma ya rufe rassansa saboda ganin hakan.

Wannan shine karo na farko da aka sanya irin wannan sharadi, a wani bangare na ceto tattalin arzikin daya daga cikin kasashe masu amfani da kudin euro.

Wakilin BBC ya ce dalilin gitta sharadin shi ne shugagbannin Turai sun yi amanna cewa akwai kudade masu yawa a Bankunan Cyprus da akai imanin na masu halalta kudaden haram ne na Rasha.

Shugaban Cypriot ya ce yarjejeniyar ce kadai hanyar dakile rugujewar harkar banki a kasar.

Karin bayani