'Yan sandan Kenya sun fatattaki magoya bayan Odinga

Kenya
Image caption An tarwatsa magoya bayan Odinga

'Yan sanda a Nairobi babban birnin Kasar Kenya sun fesa hayaki mai sa hawaye akan daruruwa magoya bayan prime minista Raila odinga

sun dai taru ne a wajen harabar kotun kolin kasar jim kadan kafin lawyoyin Mr Odinga su shigar da kara inda suke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar na wannan watan

Fira Ministan wanda abokin hamayyarsa uhuru kenyatta ya kada shi da 'yar tazara, ya yi zargin an yi magudi a zaben

Mr Odinga ya ce a yawancin runfunan zabe, kuri'un da aka kada sun haura yawan masu jefa kuri'ar da akaiwa rajista.

Karin bayani