An kai gawar Chavez makwancinta

Image caption Ana ajiye gawar Hugo Chavez a makwancinta na din din din

An kai gawar marigayi Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez wani wurin ajiya na din-din-din dake wurin ajiye kayan tarihi na Soji dake birnin Caracas.

Dubban 'yan kasar ta Venezuela ne yawancinsu sanye da jajayen tufafi, launin jam'iyyar Mr Chavez su ka yi jerin gwano a kan tituna don ganin na'urar da ta dauko akwatin gawar ta Mr Chavez.

A yayin da ake cigaba da bikin a barikin soji wurin da aka ajiye gawar ta Mr Chavez, wasu masu wakokin Kirista sun ta raira taken kasar ta Venezuela.

Karin bayani