An kama mutane 24 kan zargin fyade–'Yan sanda

Image caption 'Yan sanda a India sun kama wadanda ake zargi da fyade

'Yan sanda a kasar India sun ce sun kame fiye da mutane ashirin da hudu dangane da fyade na taron-gungu da aka yi wa wata 'yar Switzerland dake yawon bude ido a Jihar Madhaya Pradesh dake tsakiyar kasar.

'Yar yawon bude-idon ta yi wa 'yan sanda koken cewa gungun wasu mutane su takwas sun yi ma ta fyade, sun kuma lakada wa mijinta duka sun kuma kwace musu kudi da kayayyaki.

A wani lamarin kuma a Jihar ta Madhaya Pradesh, 'yan sanda sun ce sun kame wasu mutane uku wadanda aka yi zargin sun yi wa wata 'yar kasar India mai shekaru talatin da takwas fyade a kan wata motar safa a Jihar Indore a ranar Juma'a.

A watan Disambar da ta wuce, fyade na taron-gungu da aka yi wa wata daliba wadda daga bisani ta mutu ya janyo muhawara mai zafi a kan yadda ake kula da Mata a kasar India.

Karin bayani