Dubban mutane na hallara don jawabin Paparoma

Image caption Paparoma Francis zai jawabi ga dubban mabiya Catholika

Dubban mutane ne ake sa ran za su hallara nan gaba a yau Lahadi a dandalin St Peters na birnin Rome don sauraren jawabi da albarkar sabon Paparoma.

A ranar Asabar, Paparoma Francis ya ce kamata ya yi Cocin Roman Catholika ya tuna cewa an kafa shi ne don ya kula da talaka.

Ya gaya wa 'yan jarida cewar yana so shi kansa Cocin ya zamo Matalauci.

Sabon Shugaban darikar ta Catholika wanda aka zaba a ranar Laraba ya ce ya zabi ya baiwa kansa sunan St Francis Assisi wanda ya yi zamani a karni na goma sha-uku - wanda ya rinka yin aiki da alama ta zaman lafiya da talauci.

Paparoman yace, wannan ne ya sanya shi tunani da hangen wani abinda zai yi wa cocin.

Karin bayani