An kama wasu 'yan jamiyyar adawa a Zimbabwe

Shugaban 'yan adawa Morgan Tsvangirai
Image caption An kame 'yan adawa a Zimbabwe

Jam'iyyar Fira Ministan kasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai ta ce 'yan sanda sun yi awon gaba da wasu manyan mambobin jam'iyyar su uku daga cikin gidajensu a ranar lahadi

Tsohowar jamiyyar adawa ta MDC tace ba a bayyana dalilin kame mutanen ba

An kuma bada rahotan cafke Wata fitacciyar lauya mai kare hakkin dan Adam Beatrice Mtetwa, bayan data nemi ta son dalilin kame daya daga cikin mutanen

An kuma tsare Wani jami'in MDC a ranar asabar kafin a soma zaben jin ra'ayoyi akan sabon tsarin mulki

Wakilin BBC yace ba a san dalilin wannan kame kame ba, amma ana kyautata zaton hakan nada alaka da wata gwagwarmaya ta iko dake gudana a cikin gwamnatin Hadakar ta Zimbabwe

Karin bayani