Shugaban Cyprus ya dage kan saka haraji

Image caption 'Yan kasar Cyprus na dibar kudade a bankuna

Shugaban kasar Cyprus Nicos Anas-tasiads yana kokarin sasantawa cikin gaggawa da masu bayar da lamuni a kokarin rage radadin ciwon da mutane za su ji ga shawarar nan ta cirar haraji daga kudaden da suke ajiyewa a bankuna.

Batun harajin ya bakantawa 'yan kasar rai dake wani tsibiri na tekun meditteranean.

Mr Anas-tasiads ya ce shi ma ya ji ciwon wannan haraji wanda yake daya ne daga cikin sharuddan da aka gindaya na bashin euro billiyan goma da tarayyar turai da hukumar ba da lamuni ta duniya IMF za su baiwa kasar don farfado da tattalin arzikin ta.

Ya ce idan dai har ba a amince da wannan sharadi ba, to kasar za ta iya tsiyacewa.

Karin bayani