An dakatar da zirga-zirgar jiragen Dana

Image caption Dana Airlines ya yi hatsari a watan yuni 2012 a Najeriya

Ma'aikatar kula da harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya, ta dakatar da kamfanin jiragen sama na DANA Airlines daga yin zirga zirga.

Wannan dakatarwar dai ta biyo bayan wata tangarda ne da aka samu a daya daga cikin jiragen sama na kamfanin a karshen mako.

Wannan dakatarwar ta zo watanni uku bayan da gwamnatin ta dawo wa da Kamfanin sufurin jiragen lasisinsa bayan wani hadarin jirgi da daya daga cikin jiragen Kamfanin ya yi a birnin ikko.

Yanzu haka dai Kamfanin ya dakatar da zirga- zirgar a fadin kasar.

Sai dai kamfanin Dana Airlines ya ce dakatarwar ba wai kwace lasisin Kamfanin sufurin jiragen saman ba ne.

Karin bayani