Taron jam'iyyun gurguzu na duniya kan Mali

Sojojin Faransa dake jan ragamar yaki a Mali
Image caption Sojojin Faransa na jan ragamar yaki da masu fafutukar Islama a Mali

An shiga rana ta karshe, a taron da kungiyar jam'iyyun siyasa 'yan gurguzu na duniya reshen Afrika ke yi, game da kasar Mali.

Kusan jam'iyyu 30 ne masu ra'ayin gurguzu na Afrika da ma kasashen Turai ke halartar taron, wanda ake yi a jamhuriyyar Nijar.

A ranar Litinin ne kuma taron zai yi muhawara a kan halin da Mali ke ciki da kuma makomarta.

Taron 'yan gurguzun na duniya zai duba irin tsarin da ya kamata ayi, idan yakin da ake yi a Mali ya kare, da irin shirin da yakamata a yi domin maido da kasar kan tafarkin domokradiyya.

Shawarwarin da taron ya cimma game da Malin, za a gabatar da su ga shugabannin kasashen Afrika, da kuma Majalisar Dinkin Duniya.