Za a yi tattaunawa don yin zabe a Yemen

Image caption Allo a Yemen yana tallan taron tattaunawa da za ayi

Yau Litinin aka shirya za a fara wasu shawarwarin sasantawa da Majalisar Dinkin Duniya ke rufa wa baya a kasar Yemen da nufin samar da wani daftarin kundin tsarin mulki da kuma shirya zabukan da za a gudanar a badi.

Wakilai sama da dari biyar ne daga kungiyoyin siyasa daban-daban za su shiga shawarwarin wadanda ake sa ran za a shafe watanni shida ana yi.

Sai dai kuma masu tsattsauran ra'ayi masu neman 'yancin mulkin kai daga Kudancin Yemen sun ce ba za su shiga shawarwarin ba.

A ranar Lahadi sun shiga yajin aiki da zanga-zanga ta gama-gari a birnin Aden dake gabar teku.

Kasar ta Yemen ce kasar Larabawa kadai da guguwar juyin-juya halin nan ta kai ga sasantawa ta lumana.

Karin bayani