Mutane da dama sun mutu a Kano

Nigeria
Image caption Hare-haren da ake kaiwa na kara daukar sabon salo - ciki harda satar 'yan kasashen waje

Akalla mutane 20 ne aka kashe bayan da wasu jerin abubuwa suka fashe a wata tashar motar bus a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Motoci da dama ne suka kone a harin wanda aka kai a kan titin New Road da ke unguwar Sabon Gari - yankin da ke makare da mutane.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin, sai dai birnin Kano ya sha fama da hare-haren kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

Wani da ya shaida lamarin ya gayawa BBC cewa ya ga gawarwakin mutane 20 bayan fashe-fashen na ranar Litinin.

"Daya daga cikin motocin da aka kaiwa harin a cike take makil da mutane, kuma ta kone tare da wasu karin motocin hudu", kamar yadda wata mata ta shaida wa BBC.

'Mutane da dama sun mutu'

"Na gudu domin na tsira da raina inda na samu na fita daga tashar bayan fashewar abu na biyu," kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

"Ga gawarwakin mutane nan a zube a kasa."

A watan Janairun 2012, kusan mutane 200 ne suka mutu a Kano bayan wasu hare-hare da kungiyar Boko Haram ta kai a jihar.

Wannan harin ya faru ne a daidai lokacin da ake ganin al'amura sun fara daidaita a birnin - kuma wakilin BBC a jihar ya ce harin na ranar Litinin kamar daya ne tamkar da goma.

Kungiyar dai ta ce tana fada ne da gwamnatin Najeriya domin kafa tsarin shari'ar Musulunci a wasu sassan kasar.

A farkon watannan ne wata kungiyar 'yan gwagwarmayar, Ansaru, ta ce ta kashe wasu 'yan kasashen waje bakwai da ta sace a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriyar a watan Fabreru.

Karin bayani