Harin bam ya ritsa da sojoji a Maiduguri

Maiduguri
Bayanan hoto,

Akwai wuraren bincike na jami'an tsaro a sassan birnin da dama

Akalla soja daya ne aka kashe sannan wasu biyu suka jikkata bayan da wani abu ya fashe a wajen wani banki a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, a cewar hukumomi.

Mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa ta samar da zaman lafiya a Maiduguri Lieutenant Colonel Sagir Musa ya ce an kai harin ne a mahadar First Bank/Mr Bigs da ke tsakiyar birnin.

"Ina cikin banki lokacin da na ji karar fashewar wani abu.

Ko da na fito waje sai naga motar sojoji aka hara inda kuma sojojin ke tallafawa abokan aikinsu da harin ya ritsa da su," kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mutumin ya ce ya ga an ciro gawarwaki uku daga karkashin wurin da lamarin ya faru.

Wani ma'aikacin mutuware ya shaida wa Reuters cewa an kai gawar sojoji biyu da dan sanda daya a asibitin koyarwa na Maiduguri.

Bayan da aka samu tsagaita wa ta kusan wata guda, tashe-tashen hankula sun dawo a arewacin Najeriya - inda kungiyar Boko Haram ke tayar da kayar baya.

Harin na Maiduguri na zuwa ne a lokacin da 'yan sanda suka ce akalla mutane 22 ne suka mutu yayin da wasu 65 suka samu raunuka a harin kunar bakin waken da aka kai a unguwar Sabon Gari ta jihar Kano ranar Litinin.