Bayanai na kara fitowa kan harin Kano

Image caption Wani harin bam da aka kai a Najeriya

A Najeriya bayanai na cigaba da fitowa daga birnin Kano wurinda aka kai harin bam a wata tashar manyan motoci a yankin Sabon Gari irin hasarar da aka yi.

Kodayake hukumomi har ya zuwa yanzu ba su bayar da alkaluman wadanda abin ya shafa ba, wadanda suka shaida lamarin sun gaya wa BBC cewar mutane da dama ne suka rasa rayukansu, akwai kuma wadanda suka samu munanan raunuka, baya ga hasarar dunkiya mai dimbin yawa.

Wadanda suka shaida lamarin sun shaidawa BBC cewa akalla mutane sama da 20 ne suka mutu.

Rahotanni na cewa lamarin ya lalata motoci da dama.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Kano din da sauran wasu birane na arewacin Najeriya sun sha fuskantar irin wadannan hare-hare da ake zargin 'yan kungiyar nan ne ta Boko Haram ke kaiwa.

Tun harin da aka kai a Jihar ta Kano ranar ashirin ga watan Janairun bara da mutane kusan dari biyu suka rasu; ba a sake ganin hari mai muni da mutane sama da ashirin suka mutu ba.

Karin bayani