Jirgin ruwa ya nutse a gabar tekun Cross Rivers

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Cross River dake kudu maso kudancin Najeriya na cewa sama da mutane 40 ne suka rasa rayukansu a yayinda wani jirgin ruwa dauke da mutane dari da goma sha shida ya nutse a gabar mil 40 da gabar tekun Cross River.

Hukumar bada agajin gaggawa wato NEMA ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta ce gawawwaki tara ne aka samu a yayinda aka samu mutane biyu da ransu.

Kamfanin dilanci labarai na Reuters dai ya ce wasu likitoci a jihar ta Cross Rivers sun ce an kawo wasu gawwaki 45 na mutanen dake cikin jirgin.

Sai mai magana da yawon Hukumar baga agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA, Alhaji Yusha'u Shuaibu ya ce ya zuwa yanzu gawawwaki tara ne aka gano a yayinda ake ci gaba da neman sauran fasinjojin jirgin.

"Muna ci gaba da aikin ceto ko zamu samu wasu da rai.

"Bamu san inda jirgin ya fito ba kuma bamu san inda ya nufa ba." In ji Yushu'u Shaibu

Akwai dai rahotannin da ke cewa jirgin ya taso ne daga Cross Rivers a ranar Lahadi inda ya nufi kasar Gabon dake yankin Afrika ta tsakiya.

Ba kasafai a kan samu hatsarin jirgin ruwa ba a Najeriya amma dai matsalar ta yi kamari a wasu kasashen Afrika, inda a harma a shekara ta 2010 wajen mutane 138 suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin makure da fasinjoji ya kife a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

A shekarar dubu da takwas ma mutane 35 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin ruwansu ya nutse a gabar tekun Kamaru a kan hanyarsu zuwa gabon daga Najeriya.