Rayuwa na kara 'kazanta' a Mali

Mali
Image caption Oxfam ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi

Wani bincike da kungiyar agaji ta Burtaniya Oxfam ta gudanar a wani bangare na birnin Gao a arewacin Mali, ya gano cewa farashin kayan abinci na yau da kullum ya tashi da kusan kashi saba'in cikin dari.

Kungiyar ta Oxfam ta ce, yakin da ake yi a arewacin kasar ya taimaka ga wahalhalun da jama'a suke ciki.

Kasar Faransa dai na jagorantar wani farmaki a kan dakarun masu tsattsauran ra'ayin Islama wadanda a bara suka kwace iko da arewacin kasar.

"Ba a samun kayan abinci kamar masara da gero a kasuwa kwata-kwata.

Kashi tamanin cikin dari na manyan mutane sun rage addain abincin da suke ci domin samun damar ciyar da iyalansu", a cewar binciken.

Farashin man fetur ya tashi

Oxfam ta ce matakin soji da aka dauka kan kasar Mali ya sanya an rufe hanyoyi sannan 'yan kasuwa sun gudu.

Ta ce tsarin aikin banki a birnin Gao ya tabarbare, abin da ya sa kudade kadan ne suka rage a hannun mutane.

Hauhawar farashin man fetur da kuma karancinsa ya sanya an samu matukar koma-baya a fannin samar da ruwan sha da kuma wutar lantarki.

Kungiyar Oxfam ta kara da cewa yadda aka mayar da hankali kan batun yakin da ake yi, ya sa an kawar da kai daga bukatun yau da kullum na jama'a.