Shafin Twitter ya cika shekaru bakwai

Shafin Twitter
Image caption Kimanin sakonni ko tweet miliyan 400 ake aikawa a kowacce rana

Shafin internet na Twitter na bikin cika shekaru bakwai da kafuwa inda a yanzu jama'a miliyan dari biyu ke amfani da shafin.

Yayin da kimanin sakonni ko tweet miliyan dari hudu ake aikawa a kowacce rana.

Shafin wanda Jack Dorsey ya kafa a shekara ta 2006, ya zamo wata babbar hanya ta samun labarai kan al'amura na yau da kullum, ka ma daga kasuwanci, siyasa, da zaman takewa.

Jama'a daban-daban ne ke amfani da shafin da suka hada da manya da kanana, shugabannin siyasa da 'yan kasuwa.

Daga cikin fitattun mutanen da suka fara amfani da Twitter, sun hada da Sakataren kudi na Burtaniya Geporge Osborne wanda ya wallafa sakonsa na farko a shafin a ranar Laraba lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudin kasar na shekara ta 2013.

A yanzu jama'a na amfani da Twitter wurin yakin neman zabe, aika bayanai da watsa labarai, tara kudade, shirya aure, da kalubalantar shugabanni da kuma tattaunawa da fitattun mawaka kamarsu Justin Bieber - wanda a yanzu haka yake da mabiya fiye da miliyan 36 a shafin na Twitter.

Sanarwar da shugaba Obama ya yi ta nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar Amurka karo na biyu a Twitter, shi ne sakon da ya fi jan hankalin jama'a a tarihin shafin.

Karin bayani