Amurka ta ki gayyatar Najeriya taro

Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha suka saboda ahuwar da ya yi wa tsohon gwamnan Bayelsa

A Najeriya, wasu masana sun fara danganta rashin shigar da kasar cikin wasu kasashen hudu na yammacin Afirka da Amurka tayi zuwa wani taro kan demukradiya da cewa kokari ne na nuna fushin Amurkar game da afuwar da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yiwa wasu mutane ciki har da Dipriye Alamisiya tsohon gwamnan jihar Bayelsa.

Gwamnatin Amurkan dai ta gayyaci shugabannin kasashen Sierra Leone, da Senegal, da Malawi, da kuma Prime Minister Cape Verde zuwa fadar White House ne a mako mai zuwa don tattaunawa akan yadda za'a inganta dimukradiyya da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen da ke yankin.

Dr. Jibril Ibrahim, shine shugaban cibiyar raya demukradiya dake Abuja ya ce dolene gwamnati ta sauya halinta domin ta nunawa duniya da gaske take wajen yaki da cin hanci da rashawa.

"kasashen duniya na kallon yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu a kasar, muddin gwamnati ba ta tashi tsaye ba ta yi da gaske, za'a rika maida ta saniyar ware." In ji Dr. Jibril Ibrahim.

To sai dai mahukunta a Najeriya sun ce babu wani abin fushi a rashin gayyatar gwamnatin kasar zuwa wajen taron da shugaba Barak Obama ya shirya yi da wasu shugabannin kasashe hudu daga shiyyar Afirka ta yamma.

Gwamnatin Najeriyar ta ce abin farin ciki ne a ce Amurka ta yunkuro don taimakawa wadannan kasashen, saboda da Najeriyar aka yi fadi-tashi wajen kafa mulkin demokuradiyya a wadannan kasashen.

Karin bayani