Obama ya gargadi Isra'ila kan zaman lafiya

Mr Obam ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga Isra'ila
Bayanan hoto,

Mr Obam ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga Isra'ila

Shugaba Obama ya fadawa jama'ar Isra'ila cewa, za ta dore ne kawai kuma ta cigaba a matsayin kasar Yahudawa mai bin tafarkin demokuradiyya ta hanyar samar da kasar Palasdinawa mai cin gashin kanta.

Yayin da yake jawabi ga wasu dalibai a birnin Kudus, shugaba Obama yace, yanzu Isra'ila tana cikin wani hali, kuma lokaci yayi da za ta kaucewa zama saniyar ware. Obama yace,"saboda irin ci gaban fasaha da Isra'ila take da shi, abinda zai kare al'ummar Israila shi ne zaman lafiya ba tare da yin yaki ba."

Shugaba Obama ya kuma kara da cewa, kamata yayi 'yan Israila su duba irin halin da Palasdinawa suke ciki, dan su fahimci irin abinda suke fuskanta.

'Yan Palestinu dai na yin tur da gwamnatin Obama saboda a shekara ta 2009 ne, Shugaban ya yi wani jawabi a birnin Alkahira, inda ya bayyana irin matsi da kuma wahal-halun da Palestinawa ke fuskanta a kasarsu, amma shekaru hudu kenan babu abun da ya sauya.

Boren kasashen Labarawa ne dai ya sanya aka yi watsi da batun gwawarmayar Palestinawa.

A yanzu haka dai Amurka ta fi damuwa ne da kasashen Syria da kuma Iran, inda ta ce kasashen biyu sunfi ciwa Isra'ila tuwo a kwarya.

Shugaba Mahmoud Abbas dai zai so a dawo da batun gwagwarmayar da kasarsa ke yi a agendar gabas ta tsakiya, amma 'yan kasar da dama na ganin ba za ta sauya zani ba.