Obama zai kai ziyara gabar tekun Jordan

Image caption Shugaba Obama za shi gabar tekun Jordan ne bayan sa'o'i 24 a Isra'ila

Shugaba Obama zai kai ziyara gabar tekun Jordan a yau Alhamis dinan domin tattaunawa da shugaban Palestinu Mahmoud Abbas.

hugaba Obama zai kai ziyarce ce a rana ta biyu a ziyarar da ya ke kaiwa yankin, kuma zai yi wasu 'yan sa'o'i ne a Palesdinu kafin ya koma Isra'ila inda zai yi jawabin mukasuddin ziyarar tasa.

Bayan ya kwashi sa'o'i 24 a Isra'ila, shugaba Obama zai garzaya gabar tekun Jordan ne a wata takaitacciyar ziyar.

Ganin cewa Shugaba kasar ya nanata irin dankon zumuncin dake tsakanin Amurka da Isra'ila da wuya, ya sauya manufar ta sa.

'yan Palestinu dai na tur da gwamnatin na Obama saboda a shekara ta 2009 ne, Shugaba Obaman ya yi wani jawabi a birnin alkahira, inda ya bayyana irin matsi da kuma wahal-halun da Palestinawa ke fuskanta a kasarsu, amma shekaru hudu kenan babu abun da ya sauya.

Boren kasashen Labarawa ne dai ya sanya aka yi watsi da batun gwawarmayar Palestinawa.

A yanzu haka dai Amurka ta fi damuwa ne da kasashen Syria da kuma Iran, inda ta ce kasashen biyu sunfi ciwa Isra'ila tuwo a kwarya.

Shugaba Mahmoud Abbas dai zai so a dawo da batun gwagwarmayar da kasarsa ke yi a agendar gabas ta tsakiya, amma 'yan kasar da dama na ganin ba za ta sauya zani ba.

Karin bayani