Tarihin marigayi Chinua Achebe

Tarihin marigayi Chinua Achebe
Image caption Chinua Achebe ya yi fice a sassan duniya daban-daban

An haifi Chinua Achebe a shekarar 1930 - inda kuma ake masa lakabi da uwa-uba a fannin adabi a anahiyar Afrika.

Littafinsa na farko - 'Things Fall Apart' wanda aka wallafa a shekara ta 1958 - ya mayar da hankali kan tasirin mulkin mallaka ga al'ummar Afrika; yana nuna yadda aka nakasta al'adu da halayyar gargajiya ta mutane.

Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela, ya ce kasancewar da yayi tare da litattafan Chinua Achebe, ya debe masa kewar gidan yari lokacin ake tsare da shi.

Da dama daga cikin wadanda suka karanta rubuce-rubucensa, sun tabatar da hakan - musamman yadda labaran suke ratsa mutane.

Kasa da shekaru goma, itama Najeriyar da kanta sai ta fara tangal-tangal: Kabilar Chinua Achebe, ta Igbo, sun nemi ballewa daga Najeriya - dalilin da yasa kasar ta fada yakin basasa na shekara uku.

'Anthills of the Savannah'

Jim kadan bayan yakin a shekara ta 1970, ya bar Najeriya zuwa Amurka inda aka bashi mukamin Farfesa a fannin Ingilishi a jami'ar Massachusetts.

Sai dai ya koma gida a 1976, inda ya sauya akalar rubuce-rubucensa daga Turawan mulkin mallaka zuwa sabbin shugabannin Afrika.

Littafinsa mai suna 'Anthills of the Savannah', - ya samu shiga jerin litattafan da suka nemi kauytar Booker Prize - ya nuna yadda jama'a da dama a nahiyar Afrika suka dawo daga rakiyar cin hanci da mulkin kama-karya.

Sakonnin Chinua Achebe suna nuna yadda kasarsa ya gaza wurin cimma bukatun jama'a.

A cewar marigayin, matsalar kasashenmu ita ce rashin kyakkyawan shugabanci. Duk irin albarkatun da ake da su, idan babu shugabanni nagari, za a yi almubazzaranci da ita ne kawai.

Chinua Achebe ya samu mummunan rauni a hadarin mota a shekarar 1990.

Sai dai ya ci gaba da rubutu, kuma an fassara ayyukansa a kusan harsuna hamsin a sassan duniya daban-daban, wani matsayi da ake ganin ba karamar daukaka ba ce.

Karin bayani