Ana ci gaba da jimamin mutuwar Achebe

Chinua Achebe
Image caption Kungiyoyi da shugabanni da 'yan siyasa na ci gaba da nuna alhininsu

Kungiyoyi da dama da shugabanni da 'yan siyasa na ci gaba da nuna alhininsu game da rasuwar fitaccen marubucin nan na Nigeria Farfesa Chinua Achebe.

A sanarwar da ya fitar, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce za a rika tuna wa da Farfesa Achebe saboda tsage gaskiyar sa kan al'amuran da suka shafi kasa.

Jonathan ya ce duk da cewa wasu 'yan Najeriyar suna da ra'ayoyin da suka saba da na Achebe, amma babu wanda yake musu a kan kishin kasarsa.

Kungiyoyin marubuta da sauran 'yan siyasa daga ciki da wajen Nigeria, na ci gaba da nuna alhininsu kan rasuwar marigayin - wanda ya mutu bayan wata rashin lafiya a Amurka.

"Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalin Farfesa Achebe wanda ya bada gagarumar gudummawa ga Najeriya da Afrika da ma duk wani jinsin bakar fata a duniya", a cewar shugaba Goodluck Jonathan.

Wata sanarwa daga cibiyar Nelson Mandela (Nelson Mandela Centre of Memory) ta ce tana mika ta'aziyya ga iyalan Mr Achebe.

Tsohon shugaban na Afrika ta Kudu wanda ya shafe shekaru 27 a gidan yari, ya ce "kasancewar da yayi tare da litattafan Chinua Achebe, ya debe masa kewar gidan yari lokacin ake tsare da shi."