Allah ya yi wa Chinua Achebe rasuwa

Chinua Achebe
Image caption Chinua Achebe ya rasu yana da shekaru 82 da haihuwa.

Shahararren marubucin nan dan Najeriya Farfesa Chinua Achebe ya rasu yana da shekaru 82 da haihuwa, bayan ya yi fama da rashin lafiya a Amurka.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Anambra a Nigeria - inda aka haifi Mr Achebe, Mike Udah, ya shaida wa BBC cewa, jihar da Nigeria da ma nahiyar Afrika baki daya na jimamin mutuwar dansu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce za a rika tuna wa da Farfesa Achebe saboda tsage gaskiyar sa kan al'amuran da suka shafi kasa.

Daya daga cikin fitattun marubuta daga Afrika, littafinsa na Things Fall Apart da aka wallafa a shekarar 1958 - da ya mayar da hankali kan illar mulkin mallaka ga kasashen Afrika - an sayar da fiye da kofi miliyan 10.

Chinua Achebe yana kan gaba cikin wadanda suka rinka kewaya kasashen duniya domin nemawa jamhuriyar Biafra goyon baya a kasahen duniya.

Kuma wakilin BBC a Kudancin Nigeria AbdusSalam Ibrahim Ahmad, ya ce jama'ar kabilarsa ta Igbo suna girmama shi har gobe.

Tarihin marigayin

Chinua Achebe Farfesa ne na jami'ar David and Marianna Fisher a Amurka.

Hakazalika Farfesa ne kuma malami a fannin Africana Studies a jami'ar Brown, ita ma a kasar ta Amurka.

Tun shekarar 1990 yake zaune a Amurka bayan raunukan da ya samu a wani hadarin mota.

An haifi Chinua Achebe a shekarar 1930 - inda kuma ake masa lakabi da uwa-uba a fannin adabi a anahiyar Afrika.

Littafinsa na farko - 'Things Fall Apart' wanda aka wallafa a shekara ta 1958 - ya mayar da hankali kan tasirin mulkin mallaka ga al'ummar Afrika; yana nuna yadda aka nakasta al'adu da halayyar gargajiya ta mutane.

Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela, ya ce kasancewar da yayi tare da litattafan Chinua Achebe, ya debe masa kewar gidan yari lokacin ake tsare da shi.

Da dama daga cikin wadanda suka karanta rubuce-rubucensa, sun tabatar da hakan - musamman yadda labaran suke ratsa mutane.

Kasa da shekaru goma, itama Najeriyar da kanta sai ta fara tangal-tangal: Kabilar Chinua Achebe, ta Igbo, sun nemi ballewa daga Najeriya - dalilin da yasa kasar ta fada yakin basasa na shekara uku.

Karin bayani