Majalisar Cyprus za ta kara kada kuri'a

Image caption Bankunan kasar Cyprus sun kasance a rufe

Gwamnatin kasar Cyprus ta mika wasu sauye-sauyen gaggawa ga majalisar dokokin kasar a kokarin da ta ke na neman tallafi daga kasashen duniya domin taimakawa kasar daga durkushewa.

Majalisar dokokin kasar dai ta yi fatali da shirin farko da gwamnatin kasar ta mika mata wanda ya kunshi kara yawan kudin haraji da ake biya.

Kwanaki uku da suka wuce Majalisar kasar Cyprus ta yi fatali da sauyin da gwamnatin kasar ta nema wanda zai taimaka mata wajen samun tallafi daga kasashen duniya.

A yau dai 'yan majalisa za su taru ne a karo na biyu domin sake nazari a kan shirin na biyu da gwamnati ta yi.

Ana dai ganin Majalisar za ta yi nazari ne game da wani asusu na musamman da za a kafa da zai kara yawan kudin shiga daga kadarorin gwamnati.

Har wa yau Majalisar za ta yi muhawara a kan tafiyar da hannayen jari.

Amma ana ganin za a dan dakatar da kudurin da ya nemi a yi sauyi ga bakunan dake cikin matsaloli.

Wannan yunkuri dai zai taimakawa kasar tara wasu kudade ne kafin ranar Litinin lokacin da ke ganin kasar za ta fuskanci matsala saboda babban bankin Turai zai daina ba ta taimako.

Har yau dai Bankunan kasar za su ci gaba da zama a kulle inda masu ajiya ke cikin damuwa matuka a yayinda kuma kasar ke fuskantar matsin lamba daga kungiyar tarrayar Turai