Faparoma ya nemi tattaunawa da musulmi

Image caption Fafaroma Francis

Fafaroma Francis ya yi ƙira ga Chochin Katolika ya ci gaba da yunƙurinsa na tattaunawar fahimtar juna da sauran addinai musamman addinin musulunci.

Fafaroma Francis ya kuma ce, yin tattaunawa da musulmi yana da muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya.

Da yake jawabi ga jakadu a fadar Vatican, Fafaroman ya buƙaci cocin ya yi wa'azantarwa ga wadanda basu bada gaskiya ba domin yaƙar abin da ya kira mutuwar zuci da koma bayan tarbiyya a wannan zamani.

Ya kuma yi kira da a sabunta yunƙuri wajen yaƙi da talauci da kuma kare muhalli.