Burtaniya da Faransa na neman kamun kafa

Image caption Shugabanin kasashen Burtaniya da Faransa na son a baiwa 'yan tawaye makamai ne.

Burtaniya da Faransa za su ci gaba da neman amincewar sauran kasashen tarayyar Turai a kokarinsu na dage takunkumin shigo da makamai da aka sanyawa Syria domin su samu damar aikawa masu fafutuka makamai.

A karshen watan mayu mai zuwa ne ya kamata a sabonta takunkumin, amma wannu batun ne ke ya ja hankalin taron ministococin kasashen wajen tarrayar Turai a rana ta biyu a birnin Dublin.

Burtaniya da Faransa dai suna so ne su nunawa Shugaba Assad cewa da gaske suke yi a kokarin da suke na ganin a dage takunkumin da aka sanyawa kasar na shigar da makamai.

Bayan an yi tattaunawar farko a jiya juma'a, sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague da takawararsa na kasar Faransa Laurent Fabius sun ce su damu matuka game da rahotannin da ke fitowa daga birnin Aleppo na karsar Syria a wannan makon wanda ke nuni da cewa anyi amfani da makamai masu guba.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce tana binciken batun. Membobin kungiyar na tarrayar Turan dai sun amince cewa rikicin na Syria yaki ci yaki cinyewa, kuma ya kamata a kawo karshensa.

Amma yawancinsu basu amince da yunkurin Burtaniya da Faransa ba na baiwa yan tawaye makamai.

Suna dai fargabar cewa makaman na iya komawa ga hannu 'yan ta'adda inda hakan ka iya rura wutan rikicin kasar.

Wannan taro da ake yi dai ba zai dau mataki kan dage takunkumin ba, amma dai zai nuna irin kalubalen da Burtaniya da Faransa za su fuskanta a yayinda ake tunkarar wa'adain watan Mayu. Idan har kungiyar bata amince da bukatar kasashen biyu ba, akwai yiwuwar kasashen za su dau mataki ne dan kansu ne ba tare da yawun kungiyar ba.