'Yan kasar Cyprus na cikin kunci

Ministan kudi na Cyprus, Micheal Sarris yace, ana samun gagarumin cigaba a tattaunawar da ake yi tsakanin kasarsa da kungiyar tarayyar Turai da kuma asusun bada lamuni na duniya, wato IMF.

Mr Sarris ya shaidawa manema labarai cewa har yanzu akwai sauran 'yan wasu gyare gyare a shawarwarin da suka gabatar a wajan taron na yau wadanda ake bukatar yi kafin akai ga cimma yarjejeniya ta karshe.

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da kasar Cyprus ke kara kusantar wa'adin da aka bata na amincewa da yarjejeniyar da akai da ita domin ceto ta daga tsiyacewa.

Yanzu haka akwai rade-radin da ake na cewa shugaban kasar, Nicos Anastasiades, na shirin zuwa Brussels domin tattaunawa akan batun.

Wasu 'yan Cyprus din na ganin rashin cimma matsaya kan lokaci na iya jefa kasar cikin rudani, yayin wasu suka rasa ayyukansu wasu kuma suka tabka asarar kudadan ajiyarsu.