Majalisar Cyprus ta amince da sauye-sauye

Image caption Majalisar dokokin Cyprus ta amince da kudurori tara

Majalisar Dokokin Cyprus ta amince da kudurori tara domin cimma ka'idojojin kungiyar tarrayar Turai na samun tallafi.

Daya daga cikin kudurorin da Majalisar ta amince da shi, shine na yin garanbawul ga bankunan kasar.

Sanan kuma majalisar ta baiwa gwamnatin kasar hurumin tafiyar da al'umuran bankunan kasar.

A gobe ne dai Ministocin kudin kungiyar tarrayar Turai za su gana a birnin Brussels domin tattaunawa game da batun tallafin.

Kasar Cyprus ta koyi darasi sosai, mussaman irin karfin fada ajin da kungiyar tarrayar Turai ke da shi a yankin.

Har wa yau kasar na kokarin ceto Bankin Cyprus wanda a yanzu haka ke fuskantar kalubale.

Majalisar dokokin kasar ta amince ta kafa wani asusun na musamman domin tarawa gwamnatin kasar kudaden shiga.

Akwai dai wadanda ke ganin kungiyar Tarrayar Turain ba za ta amince da hakan ba.

Har wa yau Majalisar ta baiwa gwamnatin kasar ikon tafiyar da harkokin hada-hadar kudi.

A makon da ya gabata ne dai Majalisar ta yi fatali da sauye-sauyen da kungiyar tarrayar Turai da kuma Asusun bada lamuni na duniya suka bukaci kasar ta yi kafin a bata tallafi.