Kamfanin ENI zai janye daga Najeriya

Kamfanin haƙar mai na Italiya, wato E.N.I ya bayyana dakatar da dukkan ayukansa a kudancin Najeriya saboda maƙarƙashiyar da ake yi masa.

A wata sanarwa kamfanin yace, hare-haren 'yan fashin mai da ake kaiwa bututan mansa a jihar Bayelsa suna yawaita sosai.

Cikin watan jiya ne dai kungiyar nan mai ikirarin kare muradun yankin Niger Delta, mai arzikin mai, wato MEND ta dau alhakin wani hari da aka kaiwa bututn man kamfanin na E.N.I.

Kamfanonin mai a yankin Niger Delta mai arzikin mai na Najeriya sun jima suna kokawa akan fasa musu bututun mai da 'yan fashi ke yi.