Ganye: an kashe mutane 25

Image caption Taswirar Najeriya

A garin Ganye dake jihar Adamawan Najeriya, an kashe aƙalla mutane 25 waɗanda su ka haɗa har da wani fitaccen ɗan siyasa da jami'in gida fursuna da kuma wani tsohon ɗan wasan ƙwallo.

'Yan bindigar sun fasa gidan fursunan garin, sun kuma kaiwa hare-hare a ofishin 'yan sanda, da gidan babban jami'in 'yan sanda yankin, da kotu da ma wasu gine-gine da dama.

'Yan sanda sun ce, an kai hare-haren ne da manyan bidigogi da kuma rokokin harba gurneti.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da tsohon kwaminishina a jihar Adamawan, Adiel Billa.

Jihar Adamawa dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya dake fuskantar tashin hankali cikin 'yan shekarun nan.