Boris Berozovsky na Rasha ya rasu

Boris Berozovsky
Image caption Boris Berozovsky yana fama da dinbin bashi

Hamshakin dan kasuwar nan dan Rasha, da ke zaman gudun hijira a Ingila, Boris Berozovsky ya mutu a garin Surrey, yana da shekaru 67 da haihuwa.

A baya dai marigayin makusanci ne sosai ga shugaba Vladimir Putin kafin daga baya ya zama babban mai sukar suhgaban.

Kuma wannan tasa sun raba gari a shakara ta 2000.

Wakilin BBC yace marigayi Berozovsky yana cikin hamshakan attajirai 'yan kalilan da suka yi arziki bayan rushewar tsarin kwaminisanci.

Marigayin ya yi arziki ne yayin sayar da kamfanoni mallakar gwamnatin Rasha ga 'yan kasuwa cikin shekarun 1990, amma kuma daga baya ya tsunduma cikin dabaibayin bashi.

Karin bayani