Seleka ta kwace fadar shugaban kasa

Shugaba Francois Bozize
Image caption Shugaba Francois Bozize

Shekaru goman da suke wuce ne shugaba Fransuwa Bozize ya dare karagar shugabancin a wani juyin muki da akai.

Yanzu kuma akwai rahotanni dake cewa ya tsallaka zuwa janhuriyar demokradiyyar Congo, yayin da 'yan tawayen suka doshi fadar shiugaban kasar.

Ranar Asabar da yamma ne hadakar kungioyoyi uku na 'yan tawayen da suka kafa kungiyar Seleka suka kutsa kai zuwa kauyukan dake bayan garin Bangui ta arewacin birnin, inda aka ci gaba da musayar wuta a duk fadin birnin ya zuwa safiyar yau dinan.

Janhuriyar Afurka ta tsakiya dai na fama da talauci amma tana da arzukin ma'adanai sannan kuma ta na da dadaddan tarihin tashe tashen hankula.

A watan Janairu ne dai aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya amma ta rushe kafin a kai ga aiwatar da ita.

Faransa dai na da sama da 'yan kasarta dubu daya dake zaune a Bangui da kuma sojoji kadan a kasar.

Kuma tuni ta basu shawara da su zauna a gida kada su rika fita.

Karin bayani