Jami'an tsaro na sintiri a garin Ganye

Image caption Taswirar Najeriya

'Yan sanda da sojoji na ci gaba da sintiri a garin Ganye na Jihar Adamawan Najeriya bayan kashe akalla mutane 25 a wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai.

Cikin wadanda aka kashe sun haɗa har da wani fitaccen ɗan siyasa da jami'in gidan fursuna da kuma wani tsohon ɗan wasan ƙwallo.

'Yan bindigar sun fasa gidan fursunan garin, sun kuma kai hare-hare a ofishin 'yan sanda, da gidan babban jami'in 'yan sandan yankin, da kotu da ma wasu gine-gine da dama.

'Yan sanda sun ce, an kai hare-haren ne da manyan bidigogi da kuma rokokin harba gurneti.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da tsohon kwaminishina a jihar Adamawan, Adiel Billa.

Jihar Adamawa dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar tashin hankali cikin 'yan shekarun nan.