NUJ ta nemi a yi wa Boko Haram afuwa

Boko Haram
Image caption Baya ga kai hare-hare kungiyar tana yin garkuwa da 'yan kasashen waje

Kungiyar 'yan Jaridu ta kasa a Nigeria NUJ, ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta yiwa 'ya'yan kungiyar Jama'atu Ahlun Sunnah Lil da'awati wal Jihad da wasu ke kira Boko Haram a fuwa.

Shugaban kungiyar ta NUJ, Malam Muhammad Garba ya shaida wa wakilin BBC a Kaduna Nura Muhammad Ringim cewa, "afuwar ce kawai za ta kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar.

Matakin sojin da ake dauka ba zai yi wani tasiri ba illa dai kawai sake dagula al'amura," a cewarsa.

Tuni dai wasu kungiyoyi da dain dai kun mutane ciki harda mai alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar, suka yi kira ga shugaba Goodluck Jonathan, da ya yiwa 'ya'yan kungiyar afuwa.

Amma shugaban ya nace cewa ba zai yi afuwa ga mutanen da bai sani ba - yana mai kira ga 'ya'yan kungiyar da su bayyana kansu tukunna.

Sai dai a wani sako na baya-bayan nan da shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fitar, ya yi watsi da batun duk wata tattaunawa da hukumomin Najeriyar.

Ita dai kungiyar na fada ne da jami'an tsaron Najeriya a kokarin da ta ce tana yi na kafa tsarin shari'ar Musulunci, sai dai fararen hula da dama ne ke mutuwa a hare-haren da take kaiwa.

Karin bayani