Kamaru ta baiwa Bozize mafaka

kamaru
Image caption Hambararren shugaban Jamhuriyar tsakiyar Afrika, Francois Bozize

Gwamnatin Kamaru tace ta baiwa hambararren Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize mafaka ta wucin gadi.

Sanarwar ta biyo bayan rahotannin dake cewa Mr Bozize na jamhuriyar Demokradiyar Congo.

An dai tilasta masa tserewa daga kasar tasa ne bayan da 'yan tawaye suka kwace iko da Bangui, babban birnin Kasar ranar lahadi.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da juyin mulkin, ta kuma dakatar da kasar daga kasancewa mamba a kungiyar.

Tun farko dai, shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce,sojojin kasarsa akalla sha uku aka kashe a fafatawar da aka yi da 'yan tawayen.

Kasar ta Afrika ta kudu tana da sojoji kusan 400 inda suke aikin horar da rundunar sojojin kasar ta jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Karin bayani