Shugabannin Duniya sun fara tsokaci kan Afrika ta Tsakiya

Image caption Hollande ya yi kiira ga bangarori biyu masu rikici a Afrika ta Tsakiya su kafa gwamnati

Shugaba Franscois Hollande na Faransa ya yi kira ga dukkan bangarorin dake rikici a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya su kafa gwamnati, ya kuma yi kira ga kungiyoyin mutanen dake rike da makamai su girmama 'yan kasar.

'Yan tawaye sun kwace ikon Bangui babban birnin kasar tare da kwace Fadar Shugaban kasar.

Shugaba Franscois Bozize ya tsere zuwa makwabciyar kasar, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da iyalansa.

Wani Soja mai magana da yawun 'yan tawayen Kanar Nakoyo Juma ya gaya wa sashen BBC na Turanci Focus on Africa cewar Mr Bozizen ya fice daga kasar.

Yace," a yanzu mun kwace dukkan birnin, muna kuma binciken mutane a kan tituna."

Wani kakakin 'yan tawayen ya gaya wa BBC cewar abinda suke bukata shine farfado da sha'anin tsaro a duk fadin kasar.

Wani ma'aikacin jin kai a Bangui ya bayyana yanayin a matsayin wani hali na rudu da aka shiga inda ake ta wawashe kayan jama'a.

Karin bayani