Shugaban Cyprus ya kare yarjejeniyar ceton kasar

Image caption An cimma yarjejeniyar ba wa Cyprus bashin 10b Euro

Shugaban Cyprus, Nicos Anastasiades, ya kare yarjejeniyar cetar bankunan kasar daga rugujewa.

Mr Anastasiades, wanda ya sasanta cimma yarjejeniyar tare da babban bankin Turai, da kungiyar tarayyar Turai da kuma hukumar bayar da lamuni ta duniya -IMF a Brussels, ya fada a cikin wani jawabi ta Talabijin cewar yarjejeniyar nada zafi, amma kuma ita ce mafi kyau a karkashin halin da kasar ta samu kanta.

Yarjejeniyar ta kare masu kudin ajiya kalilan, to amma masu kudin ajiyar da suka kai euro fiye da dubu dari daya, da wayansu yan Rasha, na fuskantar asara babba.

Shugaban kasar ya ce a gobe za a takaita kudin da mutane za su iya fitarwa daga bankuna, bayan sun sake budewa a karon farko a cikin fiye da mako guda.

To amma ya ce za a sassata matakin sannu a hankali. Tun farko Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta yi marhabin da yarjejeniyar, tana mai cewar an raba asarar ceton daidai wa daida.

Karin bayani