An yi garkuwa da dan kasar waje a Legas

Image caption jamian tsaro a Najeriya na fama da garkuwa da mutane

A Najeriya rahotanni na cewa anyi garkuwa da wani dan kasar waje a Victoria Island dake Jihar Legas.

An rawaito Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya na cewa anyi garkuwa da wani dan kasar waje.

Sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani kan wanda akayi garkuwar da shi ko dan wacce kasa ce.

A 'yan kwanakin nan dai an yi garkuwa da 'yan kasashen waje a arewacin kasar.

A jihar Legas dai ba kasafai akan sami rahotannin yin garkuwa da mutane ba; ko daya ke garkuwa don neman kudaden fansa ya zama ruwan dare a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur dake kudancin kasar.

Haka ma yanzu masu kishin Islama na yin garkuwa da 'yan Kasashen waje a arewacin kasar, inda har yanzu akwai wasu Faransawa bakwai da aka yi garkuwar da su a yankin Kasar Kamaru dake makwabtaka da Najeriya wadanda suke hannun Kungiyar Jama'atu ahlulsunna lilda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko haram.

Sai dai wannan garkuwar da aka yi a Jihar Legas babu wanda ya dauki alhakkin ta.

An rawaito mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a wani sako da ta tura ga 'yan kasar Amurka cewa Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da garkuwar a Legas.

A 'yan kwanakin nan yan Kungiyar Ansaru sun yi ikirarin kashe wasu 'yan kasashen waje su bakwai wadanda suka yi garkuwa da su a Jihar Bauchi a wani Kamfanin gine gine.

Haka kuma a shekara ta 2012 an kashe dan birtaniya da dan italiya yayinda ake kokarin kubutar da su bayan da akayi garkuwa da su.

A Jiya Lahadi Ofishin Jakadancin Amurkar dake Legas ya fitar da sanarwar gargadi ga 'yan kasar ta Amerika a Najeriya da su yi taka tsantsan.

Karin bayani