Za a yi mulki da dokar soja a Afrika ta tsakiya

Image caption An bada sanarwar rusa kundin tsarin mulkin Afrika ta tsakiya

Rahotanni daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun ce jagoran 'yan tawayen kasar Michael Djoto-dia zai jinginar da tsarin mulkin kasar tare da rusa majalisar dokoki.

A ranar lahadi sojojinsa suka kwace Bangui babban birnin kasar abinda ya tilasta wa Shugaban kasar gudun hijira.

A wata sanarwa ga manema labarai, an rawaito Mr Djoto-dia yana cewa zai tafiyar da kasar ne da dokar soji a wannan dan tsakanin kafin a gudanar da zabe.

Gwamnatin Jamhuriyar Kamaru ta ce ta bayar da mafaka ta wani dan lokaci ga hambararren Shugaban kasar Afrika ta tsakiya, Franscois Bozize.

Kungiyar Tarayyar Afrika dai ta yi tir da juyin mulkin har ma ta dakatar da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar daga cikin kungiyar.

Mai magana da yawun 'yan tawayen Laftanar Umar Sarik, ya ce tarwatsa sojojin da suka ja daga kafin su shiga babban birnin kasar.

Yace," mun shiga birnin ne lokacinda muka fatattaki sojojin da suka ja daga a wancan bangaren.

Karin bayani