Jama'a sun farma 'yan bindiga a Bauchi

Taswirar jihar Bauchi
Image caption Bauchi ita ce jiha ta farko da jama'a suka fara daukar irin wannan mataki

Rahotanni daga jihar Bauchi a Najeriya na cewa mazauna unguwar Federal Lowcost, da ke cikin birnin Bauchi, sun yi kukan kura inda suka tunkari 'yan bindiga da suka farma unguwar, abin da ya haifar da mummunan artabu.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Muhammad Ladan, ya shaida wa BBC cewa da misalin karfe 8.30 na safe ne, 'yan bindiga suka farma unguwar.

Sai dai ya ce: "Jama'ar unguwar sun fito kwansu da kwarkwatarsu inda suka farma 'yan bindigar kafin 'yan sanda su isa wurin".

A baya ma jama'ar garin Azare sun yi irin wannnan kukan kura inda suka farma 'yan bindigar da suka kai musu hari, abinda ya haifar da mummunan bata-kashi tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro da kuma jama'ar gari.

Satar 'yan kasashen waje

Mr Ibrahim Ladan ya kara da cewa 'yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan bindigar, inda suka kama mutum guda kafin daga bisani ya mutu a asibiti.

Ya kuma ce dan sanda daya da wani farar hula sun samu rauni, amma babu wanda ya rasa ransa a bangaren jami'an tsaron da jama'ar gari.

Dama dai jama'ar garin sun cimma yarjejeniya da jami'an tsaro kan cewar za su rinka kokari su kare lafiyarsu kafin 'yan sanda su kawo musu dauki.

Jihar ta Bauchi na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda a wasu lokutan ake alakanta wa da kungiyar Boko Haram.

A watan Fabrerun da ya gabata, kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Ansaru, ta sace wasu ma'aikata 'yan kasashen waje a jihar ta Bauchi - wadanda kuma daga bisani ta ce ta kashe su.

Karin bayani