Bill Gates ya kai ziyara a Ghana

gates
Image caption Attajirin dan kasuwa, Bill Gates

Hamshakin attajirin nan na Amurka Bill Gates ya isa birnin Accra a kasar Ghana domin wata ziyara a kan batun daya shafi lafiya.

A lokacin ziyararsa Bill Gates zai duba yadda yi ma yara alluran riga kafin cutan shan inna wato polio ya samu nasara a kasar ta Ghana a yayin da a wasu kasashen ake samun matsala ciki hadda Najeriya.

A yanzu haka dai za a iya cewa Ghana tana cikin kasashen duniya suka kawar da cutar shan inna daga cikin kasarta kusan shekaru goma da suka wuce.

Haka zalika a cikin shekara ta 2002 ne, Ghana ta kawar da cutar kyanda ko kuma dussa daga cikin kasar ta.

Karin bayani