A Brazil ana shirin rage kiwon dabbobi a daji

Image caption An son rage kiwon dabbobi adaji a kasar Brazil

Babbar kungiyar dake wakiltar masu manyan shaguna a Brazil ta ce ba za ta sake sayar da naman shanu ba wadanda aka kiwata su a kungurmin daji.

Kungiyar masu manyan shaguna ta Brazil wadda ta kunshi kusan wakilai dubu uku tana fatan wannan yarjejeniyar da aka cimma za ta sanya a rage irin yadda wasu ke sabawa doka suna kiwon dabbobinsu a cikin dajin.

Sarar itatuwan da ake yi a yankin Amazon ya dan yi sauki tun daga bara, to amma mamayar filin gwamnati na cigaba da zama wata babbar matsala.

Karin bayani