Kotun Kolin Amurka na shariar auren jinsi

Image caption Gwamnatin Obama na fuskantar kiki-kaka kan auren jinsi

Kotun Koli a kasar Amurka ta fara sauraron daya daga cikin kararraki biyu da masu fafutukar goyan bayan auren jinsi daya suka shigar gabanta.

Lawyoyinsu suna kwatanta haramcin auratayyar tsakanin jinsi guda a California, da aure tsakanin wadanda launin fatar su ta bambanta, wanda kotu ta sauyawa hukunci a shekarun 1960.

Amma daya daga cikin Alkalan Kotun ya nuna dari-dari game da shari'ar; yana mai tambayar ko me yasa ma batun ya kai gaban kotu.

Garret Epps wanda wakili ne na atlatic-com kuma farfesa masanin dokokin tsarin mulki a Jami'ar Baltimore yana cikin Kotun.

Ya kuma bayyana cewa alkalin wanda ya fi mayar da kai da yin aiki da dokar jiha ba wai ta tarayya ba, zai iya murda shari'ar.

Karin bayani