Ghana ta kama 'yan China sama da 150

Image caption Ghana na kame 'yan china da ake zargin su da hakar maadanai

Hukumomi a kasar Ghana sun ce sun kame 'yan kasar China fiye da dari da hamsin a wani sabon samame da suka kai na zakulo masu hakar ma'adinai cikin kasar ba a tare da izni ba.

Jami'an hukumar kula da shigi da ficin baki ta ce za ta nemi a mayar da Mazan da Matan kasar su.

Ghana dai ita ce kasa ta biyu mafi girma a nahiyar Afrika mai arzikin gold.

'Yan kasar Ghanan ne kawai aka amince wasu su kafa kananan masana'antu na tonon ma'adinin na gold, amma hauhawar farashin gold din tun lokacinda tattalin arzikin kasashen duniya ya fara shiga wani mawuyacin hali ya janyo 'yan kasar ta China da dama wadanda ke amfani da manyan na'urori na hakar ma'adinan.

Gwamnatin ta ce hakar ma'adinan ba tare da izni ba yana yin illa ga tattalin arzikin kasar da muhalli kuma yana haddasa mutuwar mutane da dama.

Karin bayani