An tsare 'yan China da dama a Ghana

Image caption Ghana na kame 'yan china da ake zargin su da hakar maadanai

Wata kotun majistre a kasar Ghana ta bayar da umurnin tsare wasu 'yan kasar China sama da 120 bisa zargin hakar zinariya ba bisa ka'ida ba.

Jami'an shige da fice tare da sojoji da 'yan sandan kasar ne dai suka cafke 'yan Chinan a samamen da suka fara kaiwa a wasu jihohin kasar.

An kai sumamen ne domin kawar da baki 'yan kasashen waje da ke gudanar da aikin hakar zinaren da 'yan kasar ta Ghana ne kawai doka ta ba izinin yi.

Tun da farko jami'an hukumar kula da shigi da ficin baki ta ce za ta nemi a mayar da Mazan da Matan kasar su.

Ghana dai ita ce kasa ta biyu mafi girma a nahiyar Afrika mai arzikin gold.

'Yan kasar Ghanan ne kawai aka amince su kafa kananan masana'antu na tonon ma'adinin.

Sai dai hauhawar farashin zinaren tun lokacin da tattalin arzikin kasashen duniya ya fara shiga wani mawuyacin hali ya janyo 'yan kasar ta China da dama wadanda ke amfani da manyan na'urori na hakar ma'adinan.

Gwamnatin ta ce hakar ma'adinan ba tare da izini ba yana yin illa ga tattalin arzikin kasar da muhalli kuma yana haddasa mutuwar mutane da dama.

Karin bayani