Za'a bude bankuna a Cyprus

Image caption Bankin Cyprus na fuskantar kalubale

A yau da rana ne za a bude bankuna a kasar Cyprus bayan sun kasance kusan makwanni biyu a rufe.

Sai dai za'a takaitawa masu ajiya adadin kudin da za su iya karba ko kuma su tura kasashen wajen.

Kasar Cyprus dai ta dauki wannan matakin ne, a kokarinta na samun tallafi domin ceto tattalin arzikinta daga durkushewa.

An dai shigo da biliyoyin kudin euro cikin kasar domin bukatar kudin da ake da shi.

Amma dai gwamnatin kasar za ta sanya ido ga hannayen jari, saboda kada yan kasuwa sun fidda kudinsu daga kasar, musamman ma daga harkar bankuna.

Gwamnatin kasar Cyprus din ce da kuma babban bankin kasar ne wannan tsarin ba zai shafa ba.

Wannan ne dai karo na farko da za a sanya ido kan hannayen jari a yankin kungiyar tarrayar Turai.

Hakan na nuni da irin halin rashin tabbas din da ake da shi a kasar Cyprus bayan ta amince da ka'idojin karbar bashi a farko wannan makon.

Manya manyan masu ajiya a bakunan kasar biyu mafi girma za su yi asara a hanayen jarin su.